Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Daƙuwa - Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari.
Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su.
ENG; Sweet made from ground tigernuts and groundnut (A turance tana nufin daƙuwa)
Daƙwalwa - Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka.
Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu.
ENG; Large hen (A turance tana nufin daƙwalwa)
Deaf person - A turance tana nufin kurma.
Misali; Tun yana yaro ya zama kurma sakamakon ciwon baƙon dauro da ya yi.
HAU: Kurma (Tana nufin mai ɗauke da lalurar rashin ji)
Death (of prophets or saints) - A turance tana nufin faku.
Misali; Ba su san annabi ya faku ba.
HAU; Faku (Tana nufin mutuwar annabawa ko bayin Allah salihai)
Debt - A turance tana nufin bashi.
Misali; A bashi ya karɓo kayan gininsa.
HAU; Bashi (Tana nufin karɓar kuɗi ko wani abu da zimmar biya daga baya)
Debt Management Office (DMO) - Ofishin harkokin bashi
December - A turance yana nufin wata na ƙarshe a shekara.
Misali; Watan Disamba yana da kwana talatin da ɗaya.
HAU; Dismba (Wata ne na ƙarshe a shekara)
Defense Intelligence Agency (DLA) - Hukumar leƙen asiri ta soji
Delay - A turance tana nufin jinkiri.
Misali; An samu jinkiri wajen fitar da sakamakon jarrabawar saboda wasu ƙwararan dalilai.
HAU; Jinkiri (Tana nufin dakatawa ko ɗaukan lokaci)
Deleb Palm - A turance tana nufin giginya.
Misali; Gingiya tana da zaƙi da kuma maganin basir.
HAU; Giginya (Tana nufin ɗaya daga cikin 'ya'yan itaciya masu amfani ga ɗan Adam, kama daga ƙwallonta da ganyenta da ma ita kanta)