Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dauriya - Tana nufin juriya.
Misali; Tanko yana da dauriya.
ENG: Ability to endure hardship or pain (A turance tana nufin dauriya)
Daushe - Tana nufin tsohon goro.
Misali; Gwaggo ta fi son goro daushe.
ENG; Last year's kolanuts (A turance tana nufin daushe)
Dawa - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in hatsi.
Misali; Tuwon dawa na ƙara lafiya saboda tana ƙunshe da sinadarai masu inganta lafiya.
ENG: Guinea Corn (A turance tana nufin dawa)
Dawo - Tana nufin fura ba tare da nono ba.
Misali; Sakkwatawa na son dawo, sukan sha shi kodayaushe.
ENG; Ball of fura without milk (A turance tana nufin dawo)
Day After Tomorrow - A turance tana nufin jibi.
Misali; Jibi za a fara bikin kuma sai an jera sati ana yi.
HAU; Jibi (Tana nufin ranar da ke bin gobe)
Day before festival day - A turance tana nufin jajibere.
Misali; Yau jajiberen ƙaramar sallah.
HAU; Jajibere (Tana nufin kwana ɗaya kafin ranar biki (sallah ko wani shagali))
Day Of Resurrection - A turance tana nufin kiyama.
Misali; Allah SWT shi ya san ranar da kiyama za ta tashi.
HAU; Kiyama (Tana nufin ranar tsayuwa, wato ranar da za a tashi ababen halitta a yi musu hisabi)
Daɗe - Tana nufin ɗaukan lokaci mai tsaho.
Misali; Yau ɗaliban sun daɗe ba a tashe su ba.
ENG; Last Long (A turance tana nufin daɗe)
Daƙiƙa - Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi.
Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga.
ENG; Second (of time) (A turance tana nufin daƙiƙa)
Daƙiƙi - Tana nufin wanda ba ya gane karatu.
Misali; Sun ce masa daƙiƙi saboda ya faɗi jarrabawa.
ENG; Dull (A turance tana nufin daƙiƙi)