Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Danƙwalele - Tana nufin babba ko mai girma.
Misali;Na siyowa kakata danƙwalelen goro a kasuwa.
ENG;Large (A turance tana nufin danƙwalele)
Dara - Tana nufin wasa da ake yi a kan katako mai faɗi, yana kama da wasan ludo.
Misali; Da yamma ake wasan dara a majalisar.
ENG; Game like draughts (A turance tana nufin dara)
Daraja - Tana nufin muhimmanci ko tsada.
Misali; Zinare na da daraja a halin yanzu.
ENG; Worth, Value (A turance tana nufin daraja)
Darasi - Tana nufin abin da za a koya.
Misali; Malamin na koyar da darasin Lissafi.
ENG; Lesson (A turance tana nufin darasi)
Dare - Tana nufin lokacin duhu bayan faɗuwar rana.
Misali;Idan dare ya yi iska mai sanyi tana sakkowa.
ENG; Night (A turance tana nufin dare)
Dariya - Tana nufin canja yanayin fuska tare da bayyana haƙora sakamakon wani abin farin ciki ko nishaɗi.
Misali; Jama'a na ta dariya sakamakon ganin ɗan wasan barkwancin da suka yi.
ENG; Laugh (A turance tana nufin dariya)
Darkness - A turance tana nufin duhu.
Misali; Gari ya yi duhu sakamakon hadarin da ya haɗo.
HAU; Duhu (Tana nufin rashin haske)
Datti - Tana nufin dauɗa ko ƙazanta.
Misali; Kayansa sun yi datti da yawa.
ENG; Dirt (A turance tana nufin datti)
Dattijo - Tana nufin babban mutum mai kima wanda shekarunsa suka ja.
Misali; Mahaifinta dattijo ne saboda yana da dattako.
ENG; An elder (A turance tana nufin dattijo)
Daula - Tana nufin dukiya ko kayan alatu da ƙawa na duniya.
Misali; Lami tana cikin daula saboda mijinta yana da kuɗi.
ENG; Wealth (A turance tana nufin daula)