Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dandaƙa - Tana nufin daka abu har ya zama gari.
Misali; Za mu dandaƙa geron kafin mu yi kunu da shi.
ENG: Pound and Crush something (A turance tana nufin dandaƙa)
Dandi - Tana nufin yawo da rayuwa ta rashin mafaɗi.
Misali; Ta dawo daga yawon dandi ɗauke da cuta mai tsanani.
ENG: Roaming about leading a loose, carefree life (A turance tana nufin dandi)
Dandruff - A turance yana nufin farin abu da yake fitowa ta matsirar gashin kai.
Misali; Indo tana da amosani sosai a kanta.
HAU; Amosani (Wani farin abu ne da yake fitowa ta matsirar gashin kai, mai sa ƙaiƙayi da kuma lalacewar gashi.)
Danga - Tana nufin kewaye gida da karan masara.
Misali; Baba yana waje jikin danga tare da amininsa suna magana.
ENG; Cornstalk Fence (A turance tana nufin danga)
Dangantaka - Tana nufin alaƙa.
Misali;Akwai dangantaka tsakanin angon da amaryar.
ENG; Relationship (A turance tana nufin dangantaka)
Dankali - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci.
Misali; Ina son dankali musamman soyayye.
ENG; Potatoes (A turance tana nufin dankali)
Danna - Tana nufin amfani da hannu a ba da ƙarfi akan abu.
Misali; Ina ta danna ƙofar amma ta ƙi buɗuwa.
ENG; Press (A turance tana nufin danna)
Danshi - Tana nufin lema ko ruwa kaɗan da ke haddasa sanyi a guri ko jikin wani abu.
Misali; Kayan suna da danshi, ba su ƙarasa bushewa ba.
ENG; Dampness (A turance tana nufin danshi)
Danƙa - Tana nufin kamo mutum da hannu.
Misali; Ya sha danƙa a gurin 'yan sanda kuma jikinsa zai gaya masa.
ENG; Grasp With Hand (A turance tana nufin danƙa)
Danƙo - Tana nufin abu mai mannewa.
Misali; Hannayensa danƙo suke saboda ya sha alawa.
ENG; Gum (A turance tana nufin danƙo)