Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Drag Away - A turance tana nufin janye. Misali; An janye motar da ta lalace ta tare hanyar wucewa. HAU; Janye (Tana nufin jan abu daga muhallinsa)
Dribble (of saliva) - A turance tana nufin dalala. Misali; Yawu yana dalala daga bakinsa saboda nauyin bacci. HAU; Dalala (Tana nufin zubar yawu daga baki ba ƙaƙƙautawa)
Dried form of garden egg - A turance tana nufin gauta. Misali; A cikin maganin sanyin har da gauta. HAU; Gauta (Tana nufin busasshiyar ɗata)
Driver - A turance tana nufin direba. Misali; Wanda ta aura direba ne. HAU; Direba (Tana nufin matuƙin abin hawa kamar mota da babur da sauransu)
Driver ant -

A turance tana nufin kwarkwasa. 

Misali: Yara sun gujewa hanya saboda sun ga kwarkwasa suna wucewa.

HAU; Kwarkwasa (Tana nufin wasu irin ƙanana ƙwari jajaye masu cizo da ke tafiya a jere)

Driver’s Mate - A turance tana nufin karen mota. Misali; Karen mota ne mai tattara kuɗin fasinjoji ya ba wa direba. HAU; Karen Mota (Tana nufin yaron direba ko yaron mota)
Dropping Something - A turance tana nufin ɓari. Misali; Kande ta yi ɓari ɗazu, duka garin tuwon ta zubar. HAU; Ɓari (Tana nufin zubar da abu ba da gangan ba)
Drum similar to but larger than kalangu - A turance tana nufin jauje. Misali; A cikin kayan da suke kaɗawa har da jauje. HAU; Jauje (Tana nufin abin kiɗa mai kama da kalangu)
Drum similar to jauje - A turance tana nufin kolo. Misali; Malam Habu makaɗin kolo ne sama da shekaru ashirin da suka wuce. HAU; Kolo (Tana nufin nau'in abin kiɗa mai kama da jauje)
Dry -

A turance tana nufin ƙafe.

Misali: Kogin ya ƙafe tun bayan da damina ta wuce.

HAU; Ƙafe (Tana nufin abu ya bushe, babu ruwa ko danshi a ciki)

1 13 14 15 16