Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Dirt inside pocket - Tana nufin datti ko ƙura da ke taruwa a cikin aljihu. Misali; Ya wanke ƙarfamfana da ke cikin aljihunsa kafin ya sa rigar. HAU; Ƙarfamfana (A turance tana nufin ƙarfamfana)
Dirtiness - A turance tana nufin ƙazanta. Misali: Ƙazanta a muhalli na iya jawo cututtuka kala-kala. HAU: Ƙazanta (Tana nufin yanayin datti ko rashin tsafta na jiki, muhalli, ko wani abu)
Dirty - A turance tana nufin ƙazami. Misali: Rigarsa ta zama ƙazami bayan ya yi aiki a gona. HAU: Ƙazami (Tana nufin Mutum mara tsafta. Ana amfani da ita wajen bayyana mutum, wuri, ko kaya da ba su da tsabta)
Disagreement - A turance tana nufin hargitsi. Misali; An samu hargitsi a tsakanin maƙotan guda biyu. HAU; Hargitsi (Tana nufin rashin daidaito)
Disamba - Wata ne na ƙarshe a shekara.  Misali; Watan Disamba yana da kwana talatin da ɗaya. ENG; December (A turance yana nufin wata na ƙarshe a shekara)
Discipline - A turance tana nufin hora. Misali; Makarantar suna hora ɗalibai idan sun yi ba daidai ba. HAU; Hora (Tana nufin ladabtarwa)
Disclose Secret - A turance tana nufin fallasa. Misali; An fallasa abin da suka daɗe suna ƙullawa yau. HAU; Fallasa (Tana nufin tona asiri)
Disease of Fingers - A turance tana nufin kakkarai. Misali; Kakkarai yana hana bacci saboda tsananin ciwo. HAU; Kakkarai (Tana nufin ciwon Yatsa)
Disregard - A turance tana nufin fatali. Misali; Alƙali ya yi fatali da hujjojin da aka bayar. HAU; Fatali (Tana nufin watsi da abu)
District Head - A turance tana nufin hakimi. Misali; Hakimi aka naɗa shi a shekarar da ta gabata. HAU; Hakimi (Tana nufin muƙamin sarauta na shugaban lardi)
1 10 11 12 13 14 16