Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dignity -
A turance tana nufin kwarjini.
Misali; Malam Musa yana yi wa mutane kwarjini, a duk lokacin da yake magana da jama’a cikin nutsuwa da ladabi.
HAU; Kwarjini (Tana nufin mutunci, girmamawa ko ɗaukaka ta mutum)
Dila - Tana nufin wata dabba mai kama da akuya amma ta fi akuya siranta.
Misali; Akwai dila a cikin dabbobin da na gani a gidan ajiye namun daji.
ENG; Jackal (A turance tana nufin dila)
Direba - Tana nufin matuƙin abin hawa kamar mota da babur da sauransu.
Misali; Wanda ta aura direba ne.
ENG; Driver (A turance tana nufin direba)
Directions -
A turance tana nufin kwatance.
Misali: Baƙon ya tambayi kwatancen zuwa kasuwa kafin ya je.
HAU; Kwatance (Tana nufin bayanin inda za a bi domin isa wani guri)
Directorate - Hukuma, Sashe, Maikata
Directorate of Military Intelligence (DML) - Hukumar leƙen asiri ta soji
Directorate of Public Relations (DPR) - Sashen hulɗa da jama'a
Directorate of Research and Documentation (DRD) - Sashen bincike da taskance bayanai
Directors Guild of Nigeria (DGN) - Kadaurar jagorori (Daraktoci) ta Najeriya
Dirt - A turance tana nufin datti.
Misali; Kayansa sun yi datti da yawa.
HAU; Datti (Tana nufin dauɗa ko ƙazanta)