Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Despondently - A turance tana nufin jugum.
Misali; Tun da na shigo ta yi jugum a zaune.
HAU; Jugum (Tana nufin zama shiru tare da saƙe-saƙe ko tunani)
Develop into fullness - A turance tana nufin bunƙasa
Misali; Kantin ya bunƙasa yanzu suna shigo da kaya daga ƙasashen ƙetare.
HAU; Bunƙasa (Tana nufin samun gagarimin cigaba)
Diarrhoe In Children - A turance tana nufin kurga.
Misali; Tana shirin yaye ɗanta ya fara kurga.
HAU; Kurga (Tana nufin koren kashi mai kumfa wanda yaran da ake shayarwa ke yi)
Diarrhoea - A turance tana nufin gudawa.
Misali; Tun jiya yake gudawa amma ya sha magani yanzu.
HAU; Gudawa (Tana nufin yin bayan gida (kashi) akai-akai kuma mai ruwa-ruwa, a wasu lokutan ma har da ciwon ciki)
Dictionary - A turance tana nufin ƙamusu.
Misali; Dalibi ya duba ƙamus domin ya fahimci ma’anar kalmar.
HAU; Ƙamusu (Tana nufin littafin da ke ƙunshe da rubutattun kalmomi da ma'anarsu)
Diddiga - Tana nufin sauran abu ko ɓirɓishinsa.
Misali; Naman ya ƙare saura diddiga.
ENG; Remaining particles (A turance tana nufin diddiga)
Diddigi - Tana nufin bibiyar abu.
Misali; Jami'an tsaro na bin diddigin lamarin da ya faru jiya.
ENG; Tracing Something (A turance tana nufin diddigi)
Dietitians Association of Nigeria (DAN) - Ƙungiyar masana cimaka ta Najeriya
Difference - A turance tana nufin bambanci.
Misali; A tsakanin maza da mata akwai bambanci, a ɗabi'a da halitta sun sha bamban.
HAU; Bambanci (Tana nufin kasancewa ba iri ɗaya ba)
Dig - A turance tana nufin haƙa.
Misali; An haƙa rijiya a bakin masallaci.
HAU; Dig (Tana nufin yin rami)
Kishiyarta; Binne