Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Shop - A turance tana nufin kanti.
Misali; An buɗe sabon kanti a unguwarmu.
HAU; Kanti (Tana nufin gurin siyar da kayayyaki)
Short - A turance tana nufin gajere.
Misali; Na rubuta gajeren labari a shafin jaridar.
HAU: Gajere (Tana nufin mara tsayi)
Short - A turance tana nufin guntu.
Misali; Da wani guntun itace na ƙarasa girkin.
HAU; Guntu (Tana nufin mara tsayi)
Kishiyarta; Dogo/ Mai tsayi
Shoulder - A turance tana nufin kafaɗa.
Misali; 'Yan mata na rawar girgiza kafaɗa a dandali.
HAU; Kafaɗa (Tana nufin sashen jiki da ke saman hannu)
Shoulder of Meat - A turance tana nufin karfata.
Misali; Karfata na samu a rabon naman da aka yi.
HAU; Karfata (Tana nufin kafaɗar naman rago ko sa ko raƙumi da sauransu)
Showing eagerness - A turance tana nufin hanƙoro.
Misali; Tun safe yake hanƙoro, saboda za su buga ƙwallon ƙafa da abokansa.
HAU; Hanƙoro (Tana nufin nuna zaƙuwa)
Shrilling done by women to express joy - A turance tana nufin guɗa.
Misali; Matan sun kaure da guɗa a lokacin da aka shigo da amaryar.
HAU; Guɗa (Tana nufin wani salo na sarrafa ihu da mata ke yi musamman a lokutan farin ciki)
Side - A turance tana nufin gefe.
Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya.
HAU; Gefe (Tana nufin wani sashe)
Sign/Indication - A turance tana nufin ishara.
Misali; Duk wanda ya yi mugunta sai ya ga ishara kafin ya mutu.
HAU; Ishara (Tana nufin nuni ko alama)
Similarity - A turance tana nufin kama.
Misali; Yaran gidan suna kama da juna duka.
HAU; Kama (Tana nufin shige)