Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Saturday - A turance tana nufin rana ta shida a mako.
Misali; Ranar Asabar ne bikin.
HAU; Asabar (Rana ce ta shida a ranakun mako)
Sayings of prophet Muhammad SAW - A turance tana nufin Hadisi.
Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta.
HAU: Hadisi (Tana nufin maganganun manzon Allah SAW)
Scalp Disease - A turance tana nufin kora.
Misali; Yana da kora, idan ka sa hularsa za ka iya ɗauka kuma lalura ce mai wuyar sha'ani.
HAU; Kora (Tana nufin nau'in cutar fata da yake fitowa a kai)
Scheme - Shiri, Tsari
Science Teachers Association of Nigeria (STAN) - Ƙungiyar Malaman Kimiyya Ta Najeriya
Scorpion - A turance tana nufin kunama.
Misali; Kunama ce ta harbi Lado a ƙafa.
HAU; Kunama (Tana nufin ƙwaro mai cizo kuma mai dafi)
Scratch - A turance tana nufin kuje.
Misali; Amir ya faɗi ya kuje a gwuiwa.
HAU; Kuje (Tana nufin jin ciwo a saman fata)
Seal - A turance tana nufin hatimi.
Misali; Wasiƙar tana ɗauke da hatimin sarki.
HAU; Hatimi (Tana nufin wata shaida ko alama)
Search - A turance yana nufin biɗa.
Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi.
HAU; Biɗa (Tana nufin nema ko lalube)
Search - A turance tana nufin caje.
Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba.
HAU; Caje (Tana nufin duba ko ina)