Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Surround - A turance tana nufin gewaye. Misali; Ya gewaye gonarsa da kara saboda gudun dabbobi. HAU; Gewaye (Tana nufi yi wa abu ƙawanya)  
Surveyors Council of Nigeria (SURCON) - Hukumar Safiyo Ta Najeriya
Swallow - A turance tana nufin haɗiye. Misali; Ya haɗiye alawar da na ba shi. HAU; Haɗiye (Tana nufin cinyewa, ko shigar abu cikin ciki ta hanyar maƙogwaro) Kishiyarta; Amayar
Sweat - A turance tana nufin gumi. Misali; Yau ana zafi kowa ka gani gumi yake. HAU; Gumi (Tana nufin ruwan da yake tsattsafowa a jikin mutum ta saman fata musamman idan yana jin zafi ko ya yi gudu)
Sweat - A turance tana nufin jiɓi. Misali; Mara gaskiya ko a ruwa sai ya yi jiɓi. HAU; Jiɓi (Tana nufin gumi ko zufa)
Sweet made from ground tigernuts and groundnut - A turance tana nufin daƙuwa. Misali; Zan kai wa amarya daƙuwa saboda idan ta yi baƙi ta ba su. HAU; Daƙuwa (Tana nufin alawar da ake yin ta da niƙaƙƙiyar gyaɗa da aya da sikari)
Sweet pounded millet mixed with water - A turance tana nufin gumba. Misali; An raba gumba a gidan mutuwar. HAU; Gumba (Tana nufi dakakken garin gero da sikari da ruwa)
Swell - A turance tana nufin kumbura. Misali; Ƙafarsa ta kumbura lokacin da ya ji ciwo a filin ƙwallo. HAU; Kumbura (Tana nufin ƙara girma ko tashi sakamakon bigewa ko jin ciwo)
Swelling from sting or bite - A turance tana nufin ƙullutu. Misali: Yaron ya samu ƙullutu a hannunsa bayan sauro ya cije shi. HAU: Ƙullutu (Tana nufin kumburi da ke bayyana a jiki sakamakon cizon ƙwari, harbin ƙudan zuma, ko wani abu mai dafi)
Swelling or lump on the body due to illness - A turance tana nufin ƙululu. Misali: Likita ya duba ƙululun da ya fito a wuyansa domin gano abin da ya jawo shi. HAU: Ƙululu (Tana nufin kumburi ko wani ƙulli da ke fitowa a jiki sakamakon rashin lafiya ko wata cuta)
1 16 17 18 19