Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Strange - A turance tana nufin bambarakwai.
Misali; Abin ya zama bambarakwai namiji da suna Hajara.
HAU; Bambarakwai (Tana nufin abu ya kasance ba yanda ya kamata ba)
Stranger/Visitor - A turance yana nufin baƙo.
Misali; Jiya na yi baƙo da yamma.
HAU; Baƙo (Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara)
Stream - A turance tana nufin ƙorama.
Misali: Mutane suna ɗebo ruwa daga ƙoramar da ke kusa da ƙauyensu.
HAU: Ƙorama (Tana nufin ƙaramin kogi ko rafin ruwa mai gudana)
Strength - A turance tana nufin ƙarfi.
Misali: Ma'aikatan na buƙatar ƙarfi domin ɗaga kaya masu nauyi.
HAU: Ƙarfi (Tana nufin kuzarin da mutum yake da shi ko ikon aikata aiki).
Strengthen - A turance tana nufin ƙarfafa.
Misali; Malamin yana ƙarfafa wa ɗalibai gwiwa don su riƙa yin karatu sosai.
HAU; Ƙarfafa (Tana nufin maganganun da ke ba da ƙwarin gwuiwa ga wanda ake yi wa su)
Strive - A turance tana nufin dage.
Misali; Ya dage da karatu har sai da ya ci jarrabawarsa.
HAU; Dage (Tana nufin yin ƙoƙari matuƙa)
Struggle - A turance tana nufin daga.
Misali; An sha daga da shi kafin ya yadda a yi masa allurar.
HAU; Daga (Tana nufin gumurzu ko shan fama)
Struggle/Trouble - A turance tana nufin jidali.
Misali; Ya janyo wa kansa jidali tunda ya auri yarinyar nan.
HAU; Jidali (Tana nufin rikici ko ɗawainiya)
Stuttering/ Stammering - A turance tana nufin in'ina.
Misali; An ce shan ruwan tattabaru na sauƙaƙa in'ina.
HAU; In'ina (Tana nufin yin magana da ƙyar ko ana yi ana tsittsitsinkawa)
Suckling of Infant - A turance tana nufin jego.
Misali; Indo jego take shi yasa ba za ta bi mu ba.
HAU; Jego (Tana nufin shayar da jariri)