Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
State Executive Council - Majilisar Zartarwa Ta Jiha
State House of Assembly - Majilisar Dokoki Ta Jiha
State Security Service/Department of State Services (SSS/DSS) - Hukumar Tsaron Sirri Ta Ƙasa
State Universal Basic Education Board (SUBEB) - Hukuamar llimin Baidaya Ta Jiha
Stench - A turance tana nufin ɗoyi.
Misali; Kwatar ɗoyi take tun safe da aka kwashe.
HAU; Ɗoyi (Tana nufin tsananin wari)
Step by step - A turance tana nufin filla-filla.
Misali; Ya yi mana bayani filla-filla.
HAU; Filla-filla (Tana nufin daki-daki)
Step-child - A turance yana nufin agola.
Misali; Idi agola ne, mahaifina ne ya auri mahaifiyarsa bayan mahaifinsa ya rasu.
HAU; Agola (Yana nufin ɗan da mace ta zo da shi daga gidan tsohon mijinta zuwa gidan sabon mijinta)
Sterling - A turance tana nufin cakwaikwaiwa.
Misali; Na ji cakwaikwaiwa na waƙa a kan bishiya a makarantar mu.
HAU; Cakwaikwaiwa(Tana nufin tsuntsuwa ma'abociyar rera waƙa)
Sting of bee - A turance tana nufin ƙari.
Misali: An cire masa ƙari bayan kunama ta harbe shi.
HAU: Ƙari (Tana nufin dafin ƙudan zuma, maciji ko kunama da ke jawo zugi ko kumburi).
Stingy - A turance tana nufin ƙanƙamo.
Misali; Wannan mutumin ƙanƙamo ne, baya son taimakon kowa da kuɗinsa.
HAU; Ƙanƙamo (Tana nufin mutum mai rowa, wanda baya son yin kyauta)