Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) - Ƙungiyar Marubuta Wasanni Ta Najeriya
Spotted Catfish - A turance tana nufin ƙurungu. Misali: Masunci ya kama ƙurungu a kogi yau da safe. HAU: Ƙurungu (Ƙurungu wani nau’in kifi ne mai gemu da tabo a jikinsa, wanda ake samu a kogi da tafki)
Sprinkle - A turance tana nufin barbaɗa. Misali; Ya barbaɗa magani a gonarsa. HAU; Barbaɗa (Tana nufin zuzzuba abu a gurare daban-daban ba guri ɗaya ba)
Spur -

A turance tana nufin ƙaimi.

Misali; Zakara yana amfani da ƙaiminsa wajen faɗa.

HAU; Ƙaimi (Tana nufin wani abu mai kaifi da ke fitowa a ƙafar dabba (musamman zakara ko wasu tsuntsaye) da suke amfani da shi wajen kare kai ko faɗa)

Squandering - A turance tana nufin facaka. Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi. HAU; Facaka (Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba)
Squeeze Through - A turance tana nufin kutsa. Misali; Ya kutsa cikin taron don ya ga gwamnan garinsu. HAU; Kutsa (Tana nufin shiga da ƙyar)
Stab - A turance tana nufin caka. Misali; Mahaucin ya caka wuƙa a jikin naman ragon. HAU; Caka (Tana nufin soka abu da ƙarfi)
Standard Oraganization of Nigeria(SON) - Hukumar Inganci Ta Najeriya
Stare - A turance tana nufin ƙura. Misali: Ta ƙura wa zanen ido saboda matuƙar kyawunsa. HAU: Ƙura (Tana nufin kallon abu sosai ba tare da kau da ido ba)
State - A turance tana nufin jiha. Misali; An ƙirƙiri sabuwar jiha a ƙasar Najeriya. HAU; Jiha (Tana nufin wani yanki daga cikin ƙasa)
1 11 12 13 14 15 19