Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Baƙi - Tana nufin launi mai duhu.
Misali; Ina neman baƙin takalmi zan siya.
ENG; Black (A turance tana nufin baƙi)
Baƙo - Tana nufin wanda ba a sani ba ko wanda ya kawo ziyara.
Misali; Jiya na yi baƙo da yamma.
ENG; Stranger/Visitor (A turance yana nufin baƙo)
Baƙon dauro - Tana nufin cutar ƙyanda, wadda ƙananan ƙuraje ke fitowa a jiki gaba ɗaya. Idan ta yi tsamari tana haddasa kurumta, makanta da sauransu.
Misali; Cutar baƙon dauro ta yi sanadiyyar mutuwar yara da yawa a karkararmu.
ENG; Measles (A turance tana nufin ƙyanda)
Be beyond one’s reach - A turance tana nufin buwaya.
Misali; Kamfanin ya buwaya a duniya baki ɗaya.
HAU; Buwaya (Tana nufin shahara da mamaye ko ina)
Be eager -
A turance tana nufin ƙagauta.
Misali: Yaron ya ƙagauta ya je makaranta yau.
HAU; Ƙagauta (Tana nufin jin gaggawa ko tsananin son yin wani abu)
Be kind -
A turance tana nufin kyauta.
Misali: Ya kamata mu riƙa kyautata wa juna.
HAU; (Tana nufin nuna alheri, tausayi ko kyautatawa ga wasu)
Be on good terms with someone - A turance tana nufin jitu.
Misali; Sun jitu da juna shi yasa ba sa faɗa.
HAU; Jitu (Tana nufin shaƙuwa ko fahimtar juna)
Be Replete - A turance tana nufin koshi.
Misali: Ya ƙoshi sosai bayan ya ci tuwo da miya.
HAU: Ƙoshi (Tana nufin cikar ciki bayan cin abinci sosai)
Bean Cakes - A turance tana nufin ƙosai.
Misali: Ta yi ƙosai da safe domin karin kumallo.
HAU: Ƙosai (Tana nufin abincin da ake yi da markaɗaɗɗen waken da aka soya a mai)
Beard - A turance tana nufin gemu.
Misali; Ya aske gemunsa ranar Lahadi.
HAU; Gemu (Tana nufin gashin da yake fitowa a haɓar maza)