Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Business Education Exams Council (BEEC) - Hukumar jarabawar naƙaltar kasuwanci
Business Education Exams council [BEEC] - Hukumar jarabawar naƙaltar kasuwanci
Business/Affair - A turance tana nufin harka. Misali; Aboki na ya kawo min harka ta arziƙi. HAU; Harka (Tana nufin al'amura musamman na kasuwanci)
Buta - Tana nufin mazubin ruwa musamman don yin alwala. Misali; Na siyo sabuwar buta a kasuwar da na je. ENG; Kettle (A turance tana nufin buta)
Butchering - A turance tana nufin fawa. Misali; Wanda zai aure ta fawa yake. HAU; Fawa (Tana nufin sana'ar siyar da nama)
Butulu - Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa. Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa. ENG; Ungrateful (A turance tana nufin butulu)
Bututu - Tana nufin mazurari na ruwa ko iska da sauransu. Misali; Mai gyaran bututun ya zo da wuri. ENG; Tunnel/Pipe (A turance tana nufin bututu)  
Buwaya - Tana nufin shahara da mamaye ko ina. Misali; Kamfanin ya buwaya a duniya baki ɗaya. ENG; Be beyond one's reach (A turance tana nufin buwaya)
Buzu - Tana nufin mazaunin ƙasashen da ke sahara kamar Niger, Mali, Algeriya da sauransu. Misali; Mai gadin gidan buzu ne, yana tare da su tsawon shekara arba'in. ENG; Taureg (A turance tana nufin buzu)
Buzu - Tana nufin abin da ake salla a kai wanda aka yi shi da fatar akuya ko tinkiya. Misali; Malam yana sallah akan buzu a lokacin da na je. ENG; Goat or sheep skin used as prayer mat (A turance tana nufin buzu)
1 20 21 22 23