Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Bread - A turance tana nufin burodi. Misali; Da burodi muke karin kumallo kullum. HAU; Burodi (Tana nufin abin ci da ake yin sa da filawa da sikari da wasu sinadarai)
Break - A turance tana nufin karya. Misali; Yaran sun karya kujerun ajin su. HAU; Karya (Tana nufin ɓalla abu ko raba shi gida biyu)
Break Off relationship - A turance tana nufin ɓaɓe. Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya. HAU; Ɓaɓe (Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa)
Breast/Crotch of trousers - A turance tana nufin hantsa. Misali; 1. Hantsar wandons ta yage. 2. Saniyar tana da manyan hantsa. HAU; Hantsa (Tana nufin nono ko mama ko tsakiyar wando)  
Bride - A turance tana nufin amarya. Misali; Lami amarya ce. HAU; Amarya (Tana nufin macen da aka ɗaurawa aure)
Bride-groom - A turance tana nufin wanda ya yi aure. Misali; Mukhtar ango ne. Kishiyarta; Amarya HAU; Ango (Wanda aka ɗaurawa aure)
British Broadcasting Corporation (BBC) - Kamfanin yaɗa labarai na Birtaniya/Tashar labaran Bibisi
British Broadcasting Corporation (BBC) - Ƙamfanin yaɗa labarai na birtaniya/ Tashar labaran bibisi
British Common Wealth of Nations - Kadaurar kasashe Rainon Birtaniya
British Common Wealth Of Nations - Kadaurar ƙasashe rainon Birtaniya
1 17 18 19 20 21 25