Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Being Presumptuous - A turance tana nufin izgili. Misali; Bayan ya yi wa iyayensa izgili rayuwarsa rugujewa ta yi. HAU; Izgili (Tana nufin wulaƙanci ko ƙasƙantarwa musamman ga abu mai daraja)
Being Weak-Willed - A turance tana nufin karaya. Misali; Tun da majinyacin ya dena magana na karaya. HAU; Karaya (Tana nufin sakankacewa ko sallamawa)
Being wide eyed - A turance tana nufin ƙiri. Misali: Musa ya yi ƙiri da ido lokacin da ya ga abin mamaki. HAU: Ƙiri (Tana nufin buɗe ido sosai saboda mamaki, tsoro, ko kulawa)
Belching - A turance tana nufin gyatsa. Misali; Na yi gyatsa amma yunwa nake ji ba ta ƙoshi ba ce. HAU; Gyatsa (Tana nufin wata iska mai ƙara da ke fitowa daga maƙogwaro musamman idan an ƙoshi ko ana jin yunwa)
Believe - A turance tana nufin gaskata. Misali; Mun gaskata annabinmu SAW. HAU; Gaskata (Tana nufin yarda) Kishiyarta; Ƙaryata
Bell -

A turance tana nufin ƙararrawa.

Misali; An buga ƙararrawa domin ɗalibai su shiga aji.

HAU; Ƙararrawa (Tana nufin wani abu na ƙarfe da ake bugawa mai ƙara, wanda ake amfani da shi wajen sanarwa ko faɗakarwa)

Bell usually hung round donkey’s neck - A turance tana nufin gwarje. Misali; Dokinsa yana da gwarje a wuya kodayaushe. HAU; Gwarje (Tana nufin maɗauri da ake ratayawa a wuyan doki)
Bethrothal - A turance yana nufin baiko. Misali; Jiya aka yi baikon Abdullahi da Amina. HAU; Baiko (Yana nufin yarjejeniya tsakanin iyaye don aurar da 'ya'yansu)
Bi-bango - Tana nufin ruwa ya dinga biyo bango daga rufin kwano. Misali; Ɗakin ruwa yana bi-bango musamman idan ana ruwa da yawa. ENG; Water from leaky roof (A turance tana nufin bi-bango)  
Bi-da-bi - Tana nufin ɗaya bayan ɗaya. Misali; Likitan yana duba marasa lafiyan bi da bi. ENG; One after the other (A turance tana nufin bi da bi)
1 10 11 12 13 14 25