Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Agaji - Yana nufin taimako. Misali; Gwamnati ta kai agaji gidan gyaran hali da tarbiyya. ENG; Help/Assistance (A turance yana nufin taimako)
Agency - Hukuma, Ma'aikata
Agogo - Yana nufin manunin lokaci. Misali; Na siyo sabon agogo a kasuwa. ENG; Clock/Watch (A turance yana nufin agogo)
Agola - Yana nufin ɗan da mace ta zo da shi daga gidan tsohon mijinta zuwa gidan sabon  mijinta. Misali; Idi agola ne, mahaifina ne ya auri mahaifiyarsa bayan mahaifinsa ya rasu. ENG; Step-child (A turance yana nufin agola)
Agricultural Research Council of Nigeria (ARCN) - Hukumar binciken Noma Ta Najeriya
Agriculture Allied Employees’ Union of Nigeria (AAEUN) - Ƙungiyar malaman Gona Ta Najeriya
Agriculture Allied Employees’union of Nigeria (AAEUN) - Ƙungiyar Malaman Gona Ta Najeriya
Agusta - Wata ne na takwas a shekara.  Misali; Ɗalibai kan yi hutu a watan Agustan kowacce shekara. ENG; August (A turance yana nufin wata na takwas a shekara)
Ahuwa - Yana nufin sassauci ko yafiya. Misali; An yi wa masu laifin afuwa. ENG; Liniency/Pardon (A turance yana nufin sassauci ko yafiya)
Aiki - Aiki wani abu ne da mutane suke yi domin dogaro da kai. Jam'i : Ayyuka.  
1 5 6 7 8 9 19