Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Ambassador - A turance tana nufin jakada. Misali; An naɗa babanta jakadan Nageriya a ƙasar Niger. HAU; Jakada (Tana nufin wakili)
Ambulan - Tana nufin motar ɗaukan mara lafiya zuwa asibiti.  Misali; An ɗauki waɗanda suka yi hatsarin a ambulan za a kai su babban asibiti. ENG; Ambulance (A turance tana nufin motar ɗaukan mara lafiya)
Ambulance - A turance tana nufin motar ɗaukan mara lafiya.  Misali; An ɗauki waɗanda suka yi hatsarin a ambulan za a kai su babban asibiti. HAU; Ambulan (Tana nufin motar ɗaukan mara lafiya zuwa asibiti)
Ambush - A turance tana nufin fako. Misali; Shi suke fako, yana zuwa suka cafke shi. HAU: Fako (Tana nufin ɓuya don kai harin ba-zata)
Amnestic Psychology Association (APA) - Ƙungiyar masana mutuntaka Ta Amurka
Amnesty international (AI) - Hukumar Afuwa Ta Duniya /Hukumar bibiyar Haƙƙi Ta Duniya
Amosani - Wani farin abu ne da yake fitowa ta matsirar gashin kai, mai sa ƙaiƙayi da kuma lalacewar gashi. Misali; Indo tana da amosani sosai a kanta. ENG; Dandruff (A turance yana nufin farin abu da yake fitowa ta matsirar gashin kai)
An elder - A turance tana nufin dattijo. Misali; Mahaifinta dattijo ne saboda yana da dattako. HAU; Dattijo (Tana nufin babban mutum mai kima wanda shekarunsa suka ja)
Analogy / Comparison - A turance tana nufin ƙiyasi. Misali: Malamin ya yi ƙiyasi tsakanin zuciya da injin mota wajen bayyana yadda suke aiki. HAU: Ƙiyasi (Tana nufin kwatanta abu da wani abu domin bayyana kamanceceniya ko fahimtar ma’ana)
Ango - Wanda aka ɗaurawa aure. Misali; Mukhtar ango ne. Kishiyarta; Amarya ENG; Bride-groom (A turance tana nufin wanda ya yi aure)
1 9 10 11 12 13 19