Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Modeling Agencies Association of Nigeria (MAAN) - Kadaurar Ƙungiyoyin Taurari Ta Najeriya
Modesty - A turance tana nufin kunya.
Misali; Yarinyar tana da kunya da ɗa'a.
HAU; Kunya (Tana nufin kawaici ko jin nauyin aikata lefi ko haɗa ido da mutane)
Monday - Rana ce ta farko daga cikin ranakun mako.
Misali; Ranar Litinin zan fara zuwa makaranta.
HAU: Litinin
Money - A turance tana nufin kuɗi.
Misali; Duk abin da za ka siya sai ka biya kuɗi tukunna.
HAU; Kuɗi (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin cinikayya)
Monkey - A turance tana nufin biri.
Misali; Da muka je gidan ajiye namun daji mun ga biri da kura.
HAU; Biri (Tana nufin dabba mai yanayin siffar mutum)
Mother - A turance tana nufin inna.
Misali; Kande ƙanwar inna ce.
HAU; Inna (Tana nufin mahaifiya)
Motion Picture Practitioner’s Association oF Nigeria (MOPPAN) - Ƙungiyar Jaruman Fim Ta Najeriya
Motomechs & Technician Association (MOMTAN) - Ƙungiyar Injiniyoyi da Kanikawan Mota
Motor Fan - A turance tana nufin farfela.
Misali; Farfelar motar ta lalace, sai an kai gyara.
HAU; Farfela (Tana nufin fankar da ke jikin mota)
Motorcycle - A turance yana nufin babur.
Misali; A kan babur na zo makaranta yau.
HAU; Babur (Abin hawa ne mai ƙafa biyu)