Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Metal or enamel bowl -
A turance tana nufin kwano.
Misali; Ta cika kwano da shinkafa domin cin abinci.
HAU; Kwano (Tana nufin mazubin da aka yi da ƙarfe wanda ake amfani da shi wajen zuba abinci ko abin ciye-ciye ko ma dafa abinci)
Metal Roof Drain - A turance tana nufin indararo.
Misali; Mun cika gidan nan da ruwan da muka tara a indararo.
HAU; Indararo (Tana nufin hanyar da ruwa yake zubowa ta saman rufin kwano)
Millet - A turance tana nufin gero.
Misali; Bana gero zalla ya shuka.
HAU; Gero (Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai wanda ake amfani da shi wajen yin fura da kunu da sauransu)
Millet Porridge - A turance tana nufin koko.
Misali; Koko da ƙosai ɗaya ne daga cikin abincin karin kumallon Hausawa.
HAU; Koko (Tana nufin abin sha da ake yi da gero, ana dama shi da tafasasshen ruwa kamar kunu)
Mingling With Others - A turance tana nufin cuɗanya.
Misali; Na yi cudanya da mutane da dama da na je Turai.
HAU; Cuɗanya (Tana nufin mu'amala da mutane)
Ministry - Ma'aikata
Ministry of Police Affairs - Ma'aikatar Harkokin 'Ƴansanda
Misfortune/Calamity - A turance tana nufin ja'iba.
Misali; Ya ga ja'iba, bayan ya rasa ɗansa shagonsa ya kama da wuta.
HAU; Ja'iba (Tana nufin masifa ko rashin sa'a ko ibtila'i)
Misfortune/Loss - A turance tana nufin hasara.
Misali; Sun yi hasara sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a yankin su.
HAU; Hasara (Tana nufin rasa wani abu)
Kishiyarta; Riba
Missing Someone - A turance tana nufin kewa.
Misali; Idan mutum ya rasu akan kasance cikin kewarsa a kodayaushe.
HAU; Kewa (Tana nufin son gani ko kasancewa da wanda ba ya kusa ko ya rasu)