Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Maritime Workers Union of Nigeria (MWUN) - Ƙungiyar Ma'aikatan Gaɓar Tekun Najeriya
Masarrafa - Masu sarrafawa ko hada wani abu kamar abin ci ko magani domin amfanin jama'a.
Matches - A turance tana nufin ashana.
Misali; Da ashana na kunna wuta na yi girki.
HAU; Ashana (Tana nufin abin kunna wuta)
Matchet - A turance yana nufin matchet.
Misali; Ya sare bishiyar da adda yau da safe.
HAU; Adda (Makami ne mai ƙota da ake amfani da shi a gona da sauransu)
mathematics Association of Nigeria (MAN) - Ƙungiyar Masana Lissafi Ta Najeriya
Mattress - A turance tana nufin katifa.
Misali; An siyowa amarya sabuwar katifa.
HAU; Katifa (Tana nufin abin kwanciya mai laushi)
May - A turance yana nufin wata na biyar a shekara
Misali; A watan Mayu muna da gagarumin taro.
HAU; Mayu (Watan biyar kenan a shekara )
Mayu - Watan biyar kenan a shekara.
Misali; A watan Mayu muna da gagarumin taro.
ENG; May (A turance yana nufin wata na biyar a shekara)
Mazayyana - Masu yin sana'ar zayyana
Maƙiyasta - Masu yin ƙiyasin ƙiɗiɗɗiga, kamar na adadin abubuwa da za a yi amfani da su tun daga farko farko har zuwa ƙarshen aikin gini da makamantansu.