Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Make beautiful -

A turance tana nufin ƙawata.

Misali: Ta ƙawata ɗakin bikin ta da furanni da fitilu masu launi.

HAU: Ƙawata (Tana nufin gyara wani abu don ya zama mai kyau ko abin kallo)

Make Slushy - A turance tana nufin caɓa. Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai. HAU; Caɓa (Tana nufin yin ado da yawa)
Makimanta - Masu kimanta darajar ƙasa ko gida, musamman wajen kimanta darajar muhalli.
Male Hyena - A turance tana nufin kure. Misali; Auwalu ya kamo kure, da shi yake wasa ranar kasuwa. HAU; Kure (Tana nufin namijin kura)
Malicious Act - A turance tana nufin Ƙeta. Misali: Ƙeta ce raba makaho da sandarsa. HAU: Ƙeta (Tana nufin aikata wani mummunan abu da nufin cutarwa ko yin sharri ga wani)
Man’s charm worn around the arm - A turance tana nufin kambu. Misali; Gaba ɗaya mafarautan suna ɗauke da kambu a hannunsu. HAU; Kambu (Tana nufin wani nau'in surkulle da maza ke ɗaurawa a hannu musamman mafarauta da 'yan dambe)
manufacturers Association of Nigeria (MAN) - Ƙungiyar Kamfanonin Ƙere-Ƙere-Ta Najeriya
Marawaita - 'Yan rahoto, masu hadawa da kawo rahoto game da wani abu ko wata ma'aikata.
March - A turance yana nufin wata na uku a shekara  Misali;Adamu zai koma sabon gidansa a watan Maris. HAU; Maris (Wata ne na uku a shekara)
Maris - Wata ne na uku a shekara.  Misali;Adamu zai koma sabon gidansa a watan Maris. ENG; March (A turance yana nufin wata na uku a shekara)
1 2 3 4 9