Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Karkara - Tana nufin ƙauye.
Misali; Mutanen karkara suna da karamci matuƙa.
ENG; Rural Area (A turance tana nufin karkara)
Karkarwa - Tana nufin rawar da jiki yake yi sakamakon zazzaɓi ko jin sanyi.
Misali; Idan ba ka sa rigar sanyi ba za ka yi karkarwa saboda yau akwai matuƙar sanyi.
ENG; Shivering (A turance tana nufin karkarwa)
Karkashi - Tana nufin ganyen da ake miya da shi, yana da yauƙi sosai.
Misali; Tuwo zan dafa da miyar karkashi yau.
ENG; Herb used in making soup (A turance tana nufin karkashi)
Karmami - Tana nufin ganyen dawa.
Misali; Da ya bi shi da gudu, cikin karmami ya shige.
ENG; Leaves of Guinea-corn (A turance tana nufin karmami)
Karo - Tana nufin haɗuwar ba-zata.
Misali; Karo na yi da bango saboda duhu, shi yasa goshi na ya kumbura.
ENG; Collision (A turance tana nufin karo)
Karo-karo - Tana nufin haɗaka ma'ana a haɗo wancan da wannan guri ɗaya.
Misali; Za mu yi masa karo-karo ya siyi babur ya kama sana'a.
ENG: Seeking contribution from various people (A turance tana nufin karo-karo)
Karofi - Tana nufin rami mai ɗauke da ruwan da ake rina tufafi.
Misali; Na taɓa ganin karofi a marinar da ke unguwar Ƙofar Mata.
ENG; Dye-pit (A turance tana nufin karofi)
Karsana - Tana nufin matashiyar saniya wadda ba ta taɓa haihuwa ba.
Misali; Naman karsana yana da taushi da sauƙin dahuwa.
ENG; Young cow who has not yet given birth (A turance tana nufin karsana)
Kartagai - Shugabannin caca, wanda suka mallaki kaya da ma wuri ko gidajen yin cacar.
Karuwa - Tana nufin mace mai zaman kanta.
Misali; Ku karanta ƙissar karuwa da karen da ta ba wa ruwa, akwai darasi.
ENG; Prostitute (A turance tana nufin karuwa)