Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Karaya - Tana nufin sakankacewa ko sallamawa.
Misali; Tun da majinyacin ya dena magana na karaya.
ENG; Being Weak-Willed (A turance tana nufin karaya)
Kare - Tana nufin dabba mai ƙafa huɗu da jela kuma mai haushi.
Misali; Tun tsakar dare nake jin haushin kare har asuba.
ENG; Dog (A turance tana nufin kare)
Kishiyarta; Karya
Karen Mota - Tana nufin yaron direba ko yaron mota.
Misali; Karen mota ne mai tattara kuɗin fasinjoji ya ba wa direba.
ENG; Driver's Mate (A turance tana nufin karen mota)
Karfasa - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'ikan kifi.
Misali; Malam Idi yana soya karfasa ne bayan la'asar.
ENG; Tilapia (A turance tana nufin karfasa)
Karfata - Tana nufin kafaɗar naman rago ko sa ko raƙumi da sauransu.
Misali; Karfata na samu a rabon naman da aka yi.
ENG; Shoulder of Meat (A turance tana nufin karfata)
Kargo - Tana nufin ɗaya daga cikin nau'ikan bishiya mai matuƙar amfani wajen yin magunguna daban-daban.
Misali; Garin sassaƙen kargo na maganin ciwon haƙori, ciwon kunne da ciwon ciki.
ENG; A tree whose bark is used as medicine (A turance tana nufin kargo)
Karimi - Tana nufin mutum mai girma da darajta mutane tare da kyautata musu.
Misali; Masha Allah ai Alhaji karimi ne ƙwarai da gaske.
ENG; Generous (A turance tana nufin karimi)
Karin Magana - Tana nufin zance na hikima mai ƙunshe da nuni ko habaici wanda ake yi don azanci ko huce haushi.
Misali; Darasin da malamin Hausa ya koyar yau shi ne karin magana.
ENG; Proverb (A turance tana nufin karin magana)
Karkanda - Tana nufin ɗaya daga cikin dabbobin daji mai matuƙar ƙarfi.
Misali; Ba a ganin karkanda sai a ƙungurmin daji.
ENG; Rhinoceros (A turance tana nufin karkanda)
Karkara - Karkara wani yanki ne na gari wanda yake ke6antaccen waje ne da yakje da karancin jama'a da kuma yake da yawan gonaki da filaye.