Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kanti - Tana nufin gurin siyar da kayayyaki.
Misali; An buɗe sabon kanti a unguwarmu.
ENG; Shop (A turance tana nufin kanti)
Kantoma - Tana nufin mai riƙon ƙwaryar shugabancin ƙaramar hukuma.
Misali; An naɗa baban su Sharif kantoma a ƙaramar hukumar Dala.
ENG; Local Authority Administrator (A turance tana nufin kantoma)
Kanumfari - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan ƙamshi.
Misali; Shayi idan an sa kanumfari ya fi daɗi.
ENG; Clove (A turance tana nufin kanumfari)
Kanwa - Tana nufin wani nau'in gishirin tabki mai ƙunshe da sinadarin sodium a ciki.
Misali; Ki ɗan jefa kanwa a waken don ya yi laushi da wuri.
ENG; Potash (A turance tana nufin kanwa)
Karaf - Tana nufin ba zato ba tsammani.
Misali; Ta yi karaf ta kamo shi kafin ya gudu.
ENG; Suddenly (A turance tana nufin karaf)
Karaga - Tana nufin kujerar mulki ko sarauta.
Misali; Sarki yana zaune a kan karaga tun safe.
ENG; Throne (A turance tana nufin karaga)
Karantar - Tana nufin koyarwa.
Misali; Ya karantar da mu darussa masu yawa.
ENG; Teach (A turance tana nufin karantar)
Karate Fedaration of Nigeria (KFN) - Hukumar Wasan Kareti Ta Najeriya
Karatu - Tana nufin ambaton abinda aka rubuta.
Misali; Tun safe ɗaliban suke karatu ba ƙaƙƙautawa.
ENG; Reading (A turance tana nufin karatu)
Karauka - Tana nufin babbar hanya ko babban titin da ke sa-da jihohi.
Misali; Bin karauka sai manyan direbobi.
ENG; High Way (A turance tana nufin karauka)