Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kammala - Tana nufin gamawa. Misali; Idan kun kammala aikin da na ba ku sai ku tafi gida. ENG; Complete (A turance tana nufin kammala) Kishiyarta; Fara/Farawa
Kamɓori - Tana nufin ɓawo ko kwanson ƙwai. Misali; Ana haɗa hoda wacce mata ke shafawa da kamɓori. ENG; Egg Shell (A turance tana nufin kamɓori)
Kan ƙuda - Tana nufin ɗan ƙanƙani. Misali; In dai akwai ɗigon da ya kai kan ƙuda na shirka a zuciya, to ta ɓaci. ENG; Tiniest Amount (A turance tana nufin kan ƙuda)
Kan-gado - Tana nufin hankali ko fahimta. Misali; Yaron yana da kan-gado ainun. ENG; Common Sense (A turance tana nufin kan-gado)
Kananzir - Tana nufin makamashin da ake amfani da shi wajen girki da kunna fitila. Misali; Zamani ya sa an dena amfani da kananzir sosai. ENG; Kerosene (A turance tana nufin kananzir)
Kanari - Tana nufin wani nau'in tsuntsu ma'abocin rera waƙa. Misali; Tun asuba nake jin kukan kanari a kan bishiyar gidan nan. ENG; Canary (A turance tana nufin kanari)
Kandagarki - Tana nufin kariya. Misali; Ya yi wa kansa kandagarki don ya san zai daku. ENG; Protection (A turance tana nufin kandagarki)
Kangara - Tana nufin fitina ko gagara ko rashin ji. Misali; Shagwaɓa yara na sa su a halin kangara. ENG; Become difficult to control (A turance tana nufin kangara)
Kango - Tana nufin ginin da ba a kammala ba. Misali; Har yanzu ginin kango ne ba a ƙarasa ba. ENG; Uncompleted Building (A turance tana nufin kango)
Kankana - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan maramari mai ɗauke da ruwa sosai a ciki. Misali; Kankana ta fi yawa a cikin kayan marmarin da muka siyo. ENG; Watermelon (A turance tana nufin kankana)
1 4 5 6 7 8 23