Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kallo - Tana nufin duba izuwa wani abu.
Misali; Yana shigowa ɗakin taron kowa ya bi shi da kallo.
ENG; Watch (A turance tana nufin kallo)
Kama - Tana nufin shige.
Misali; Yaran gidan suna kama da juna duka.
ENG; Similarity (A turance tana nufin kama)
Kama - Tana nufin riƙe abu da hannu.
Misali; Jami'an tsaro sun kama masu lefi da yawa a wannan makon.
ENG; Catch (A turance tana nufin kama)
Kamanta - Tana nufin kwantantawa.
Misali; Alƙalin yana kamanta adalci a shari'o'insa.
ENG;Compare (A turance tana nufin kamanta)
Kamasho - Tana nufin wani kaso na kuɗi da ake samu bayan an yi ciniki.
Misali; Mukan samu kamasho a kowanne kaya da aka siyar a shago.
ENG; Comission on things sold (A turance tana nufin kamasho)
Kambi - Tana nufin wani abu mai kamar hula da sarakuna da 'ya'yansu ke sa wa.
Misali; Sarkin yana sanye da kambi a lokacin da aka yi taron.
ENG; Crown (A turance tana nufin kambi)
Kambu - Tana nufin wani nau'in surkulle da maza ke ɗaurawa a hannu musamman mafarauta da 'yan dambe.
Misali; Gaba ɗaya mafarautan suna ɗauke da kambu a hannunsu.
ENG; Man's charm worn around the arm (A turance tana nufin kambu)
Kamfani - Tana nufin ma'aikata mai ɗauke da mutanen da suke aiki a ƙarƙashinta.
Misali; Alhaji Mudi ya gina sabon kamfani a karkararsu.
ENG; Company (A turance tana nufin kamfani)
Kamfata - Tana nufin ɗiban abu da yawa.
Misali; Idan ba ka zuba musu abincin ba kamfata za su yi.
ENG; Take much of (A turance tana nufin kamfata)
Kamili - Tana nufin nagartaccen mutum mai kyawawan halaye.
Misali; Malam Musa kamili ne.
ENG; Gentle person (A turance tana nufin kamili)