Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kaki - Tana nufin majinar da ake fitarwa daga maƙogwaro.
Misali; Mura ta sa yana ta kaki.
ENG; Phlegm From Throat (A turance tana nufin kaki)
Kaki - Tana nufin saƙar zuma.
Misali; Zumar mai kyau ce don a cikin kaki take.
ENG; Bees-wax (A turance tana nufin kaki)
Kakide - Tana nufin kitsen da ake samu a jikin nama musamman bayan an soya.
Misali; Ina son babbar sallah ta zo don in samu kakide bayan an soya nama.
ENG; Meat Fat (A turance tana nufin kakide)
Kakkarai - Tana nufin ciwon Yatsa.
Misali; Kakkarai yana hana bacci saboda tsananin ciwo.
ENG; Disease of Fingers (A turance tana nufin kakkarai)
Kakkaɓe - Tana nufin goge datti ko ƙura.
Misali; Sai da na kakkaɓe ƙura a kan kujerar kafin na zauna.
ENG; Shake dust off something (A turance tana nufin kakkaɓe)
Kalaci - Tana nufin abinci, na safe ko na rana ko na dare.
Misali; Idan na gama kalaci za mu je dubiya.
ENG; Any Meal (A turance tana nufin kalaci)
Kalami - Tana nufin zance ko magana.
Misali; Ya iya kalami mai daɗi shi yasa mutane ke son shi.
ENG; Words/Speech (A turance tana nufin kalami)
Kalanda - Tana nufin jadawalin da ke ƙunshe da watanni goma sha biyu na shekara.
Misali; Sabuwar kalandar muslunci ta fito.
ENG; Calendar (A turance tana nufin kalanda)
Kalangu - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kaɗe-kaɗe na gargajiya.
Misali; 'Yan mata na son kiɗan kalangu matuƙa.
ENG; Variable-tone Drum (A turance tana nufin kalangu)
Kallabi - Tana nufin ɗan kwali ko fatala.
Misali; Ƙanwata ta iya ɗaura kallabi.
ENG; Woman's Head-tie (A turance tana nufin kallabi)