Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kyankyaso - Tana nufin wani ƙaramin ƙwaro da ake samu a gida ko wurare masu datti musamman banɗaki. Misali: An ga kyankyaso a cikin ɗakin girki. ENG: Cockroach (A turance tana nufin kyankyaso)
Kyanwa -

Tana nufin dabba mai kama da damisa ƙarama wadda ake kiwo a gida.

Misali: Kyanwar gidanmu tana kama ɓeraye.

ENG: Cat (A turance tana nufin kyanwa).

Kyarkyara -

Tana nufin ƙarar da kaza ke yi kafin ta yi ƙwai.

Misali: Na ji kyarkyarar kaza a bayan gida.

ENG: Cackling of hen before laying egg (A turance tana nufin kyarkyara).

Kyarma -

Tana nufin rawar jiki saboda sanyi, tsoro ko rashin lafiya.

Misali: Yaron yana kyarma saboda tsananin sanyi.

ENG: Shivering (A turance tana nufin kyarma).

Kyat -

Tana nufin abincin zaƙi da ake yi da fulawa, sukari da ƙwai da sauran kayan haɗi.

Misali: Mun ci kyat a wajen bikin ranar haihuwar abokinmu.

ENG: Cake (A turance tana nufin kyat)

Kyauro -

Tana nufin sandar kibiya da ake amfani da ita wajen harbi.

Misali: Maharbin ya gyara kyauron kibiyarsa.

ENG: Arrow Shaft (A turance tana nufin kyauro).

Kyauta -

Tana nufin nuna alheri, tausayi ko kyautatawa ga wasu.

Misali: Ya kamata mu riƙa kyautata wa juna.

ENG: Be kind (A turance tana nufin kyauta).

1 31 32 33