Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kwazari -
Kwazazzabo -
Tana nufin rami mai zurfi da ruwa ya haƙa a ƙasa ta hanyar wucewa na tsawon lokaci.
Misali: Ruwan sama mai ƙarfi ya ƙara faɗaɗa kwazazzabo a gefen hanya.
ENG; Water-cut channel / gorge (A turance tana nufin kwazazzabo)
Kwaɓa - Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya.
Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin.
ENG; Mix Something (A turance tana nufin kwaɓa)
Kwaɗayi - Tana nufin tsananin son cin abu ko yin abu.
Misali; Tun da ta fara kwaɗayi na san tana da juna biyu.
ENG; Craving/ Yearning (A turance tana nufin kwaɗayi)
Kwaɗo - Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa.
Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu.
ENG; Frog (A turance tana nufin kwaɗo)
Kwikwiyo - Tana nufin jaririn kare.
Misali: Yara suna wasa da kwikwiyo a farfajiyar gida.
ENG; Puppy (A turance tana nufin kwikwiyo)
Kwiɓi - Tana nufin ɓangaren jikin mutum da ke tsakanin ƙirji da kwankwaso, wato gefen ciki.
Misali: Ya riƙe kwiɓinsa saboda ciwon da ya ji bayan ya faɗi.
ENG; Side of the body between thorax and hips (A turance tana nufin kwiɓi)
Kyakkyawa - Tana nufin abu ko mutum mai kyau, mai jan hankali ko mai kyau a ido.
Misali: Aisha kyakkyawa ce sosai.
ENG; Beautiful (A turance tana nufin kyakkyawa)
Kyamara - Tana nufin na’urar da ake amfani da ita wajen ɗaukar hoto ko bidiyo.
Misali: Umar ya sayi sabuwar kyamara domin ɗaukar hoto.
ENG: Camera (A turance tana nufin kyamara).
Kyandir - Tana nufin abin da ake kunna wa domin samar da haske, musamman idan babu wuta.
Misali: Mun kunna kyandir saboda wutar lantarki ta ɗauke.
ENG: Candle (A turance tana nufin kyandir).