Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kwartanci -

Tana nufin yin hulɗar soyayya ta haram tsakanin mace ko namiji musamman idan macen ta kasance matar aure ce.

Misali: Addini da al’ada suna hani da aikin kwartanci.

ENG; Adultery (A turance tana nufin kwartanci)

Kwarto -

Tana nufin masoyi ko wanda ake hulɗar soyayya da shi ba tare da aure ba.

Misali: Jiya da yamma an kama kwarto a bayan layinmu ya shiga gidan wani matafiyi.

ENG; Lover / Mistress (A turance tana nufin kwarto)

Kwata -

Tana nufin riga mai kauri da ake sawa domin kariya daga sanyi ko ado.

Misali: Aliyu ya sa kwat saboda sanyi ya yi yawa da safe.

ENG; Coat (A turance tana nufin kwat)

Kwata -

Tana nufin ruwan datti ko mashigar da datti da najasa da tarkace ke bi.

Misali: An gyara kwata domin hana ruwan datti yawo a unguwar.

ENG; Sewage (A turance tana nufin kwata)

Kwata -

Tana nufin rubu’in yadi ko wani ɓangare ɗaya cikin huɗu na awo.

Misali: Ta sayi kwata na yadi domin ɗinka gyale.

ENG; Quarter of yard (A turance tana nufin kwata)

Kwata-kwata -

Tana nufin gaba ɗaya ko baki ɗaya ba tare da saura ba.

Misali: Ruwan sama ya tsaya kwata-kwata kafin mutane su fara fita waje.

ENG; Completely (A turance tana nufin kwata-kwata)

Kwatance -

Tana nufin bayanin inda za a bi domin isa wani guri.

Misali: Baƙon ya tambayi kwatancen zuwa kasuwa kafin ya je.

ENG; Directions (A turance tana nufin kwatance)

Kwatanta -

Tana nufin auna kamanceceniya ko bambancin da ke tsakanin abubuwa biyu ko fiye.

Misali: Malam ya umurci ɗalibai su kwatanta rayuwar da da ta yanzu.

ENG; Compare (A turance tana nufin kwatanta)

Kwatarniya - Tana nufin babbar tukunyar ƙasa mai faɗin baki wadda ake ajiyar ruwa ko hatsi a ciki. Misali: Kaka ta cika kwatarniya da ruwa domin amfanin gida. ENG; Large wide-mouthed earthenware pot (A turance tana nufin kwatarniya)
Kwatashi -

Tana nufin saman gida mai hawa-hawa, wato bene.

Misali: Iyalan suna zaune a kwatashi yayin da shagunan suke ƙasan ginin.

HAU; Upper storey of a house (A turance tana nufin kwatashi)

1 29 30 31 32 33