Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kwararo -

Tana nufin ƙaramin titi ko hanyar da ke tsakanin gine-gine, wadda ake iya wucewa.

Misali; Yara suna wasa a cikin kwararo na unguwa.

ENG; Alley (A turance tana nufin kwararo)

Kwari -

Tana nufin akwati ko jakar da ake ɗaukar kibiyoyi a ciki lokacin harbin kibiya.

Misali; Maharbin ya ɗauki kwari cike da kibiyoyi.

ENG; Quiver (A turance tana nufin kwari)

Kwari -

Tana nufin gangare ko ramin da ruwa ke taruwa ko ya wuce

Misali; Ruwa yana gudana a cikin kwari bayan damina.

ENG; Valley (A turance tana nufin kwari)

Kwarjini -

Tana nufin mutunci, girmamawa ko ɗaukaka ta mutum.

Misali; Malam Musa yana yi wa mutane kwarjini,  a duk lokacin da yake magana da jama’a cikin nutsuwa da ladabi.

ENG; Dignity (A turance tana nufin kwarjini)

Kwarkwaro - Tana nufin abin da ake naɗa zare a jikinsa yayin aikin saƙa ko ɗinki.   Misali: Kaka ta ɗora zare a kan kwarkwaro kafin ta fara saƙa tufafi. ENG; Spindle for thread (A turance tana nufin kwarkwaro)
Kwarkwasa - Tana nufin jan hankali ta hanyar magana ko juya sassan jiki. Misali: Sani yace budurwarsa na yawan yi masa kwarkwasa a lokacin da ya je hira. ENG; Flirting (A turance tana nufin Kwarkwasa)
Kwarkwasa -

Tana nufin wasu irin ƙanana ƙwari jajaye masu cizo da ke tafiya a jere. 

Misali: Yara sun gujewa hanya saboda sun ga kwarkwasa suna wucewa.

ENG; Driver ant (A turance tana nufin kwarkwasa)

Kwarkwashi -

Tana nufin farin ɓawon da ke fitowa a matsirar gashin kai wanda ke lalata gashi da karairaya shi.

Misali: Ta sayi maganin kwarkwashi domin rage yawan lalacewar da gashin kanta ke yi.

ENG; Dandruff (A turance tana nufin kwarkwashi)

Kwarkwata -

Tana nufin ƙananan ƙwari da ke rayuwa a gashin kai ko jiki suna tsotsar jini.

Misali: Indo ta shafa wa yaranta maganin kashe kwarkwata a kansu.

ENG; Louse / Lice (A turance tana nufin kwarkwata)

Kwarmato -

Tana nufin yawan faɗin sirri ko magana ba tare da ɓoye abu ba.

Misali: An hana shi shiga taro saboda halinsa na kwarmato.

ENG; Blabbing (A turance tana nufin kwarmato)

1 28 29 30 31 32 33