Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kafiri - Tana nufin wanda ba musulmi ba.
Misali; Duk wanda ya yi sallah ba tare da alwala ba kafiri ne.
ENG; Non-Muslim (A turance tana nufin kafiri)
Kaftani - Tana nufin taguwa mai faffaɗan hannu.
Misali; Yayin kaftani ake yi yanzu.
ENG; Caftan (A turance tana nufin kaftani)
Kai-dauki - Taimakawa ko kai agaji domin ceto.
Kaifi - Tana nufin ƙarfin da zai iya yanka.
Misali; Wuƙar tana da kaifi sosai don ta yanke ni.
ENG; Sharpness (A turance tana nufin kaifi)
Kaigama - Tana nufin ɗaya daga cikin sarautun gargajiya.
Misali; An naɗa shi sarautar kaigama yau da safe.
ENG; A traditional title (A turance tana nufin kaigama)
Kaji - Tana nufin jam'in kaza.
Misali; An soya kaji za a yi mana miya da su.
ENG; Chicken/Hen (A turance tana nufin kaji)
Kakabi - Tana nufin mamaki ko al'ajabi.
Misali; Tun jiya muke ta kakabi saboda abin ya girmama.
ENG; Suprise/Wonder (A turance tana nufin kakabi)
Kakaki - Tana nufin abin busa na ƙarfe wanda sarki kaɗai ake busawa.
Misali; Da ka ji kakaki to sarki ya fito daga fada.
ENG; Long metal horn blown in honour of an Emir (A turance tana nufin kakaki)
Kakari - Tana nufin ƙarar da ke fitowa sakamakon toshewa ko yanka maƙogwaro, musamman idan an yanka dabba.
Misali; an daɗe da yanka saniyar amma har yanzu tana ta kakari.
ENG; Gasping noises made by animal whose throat has been cut (A turance tana nufin kakari)
Kaki - Tana nufin kayan sojoji.
Misali; Dole ne ka ji tsoron mai kaki don ka san soja ba abin wasa ba ne.
ENG; Khaki Cloth (A turance tana nufin kaki)