Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kwano -

Tana nufin mazubin da aka yi da ƙarfe wanda ake amfani da shi wajen zuba abinci ko abin ciye-ciye ko ma dafa abinci.

Misali; Ta cika kwano da shinkafa domin cin abinci.

ENG; Metal or enamel bowl (A turance tana nufin kwano)

Kwanta -

Tana nufin shimfiɗa jiki a ƙasa ko kan gado don hutawa ko yin bacci. 

Misali; Bayan ya wuni yana aiki, ya kwanta a gado don ya  huta.

ENG; Lie down (A turance tana nufin kwanta)

Kwantai -

Tana nufin abinci ko kayan da suka lalace ko suka ragu a kasuwa waɗanda ba a sayar ba.

Misali; A'isha takan siyar da abincinta a kullum amma yau ta yi kwantai.

ENG; Perishable foodstuffs left unsold (A turance tana nufin kwantai)

Kwanto -

Tana nufin ɓoye kai ko ɓoye jiki domin kai hari.

Misali; Maharbi ya yi kwanto zai harbi gada.

ENG; Hiding oneself for ambush (A turance tana nufin kwanto)

Kwantsa -

Tana nufin datti mai kamar majina da ke taruwa a ido yayin barci musamman idan idon yana ciwo.

Misali; Yaron ya goge kwantsa daga idonsa da safe.

ENG; Mucus that collects in the eye during sleep (A turance tana nufin kwantsa)

Kwanya -

Tana nufin ƙashi na kai wanda ke rufe ƙwaƙwalwa.

Misali; Likita ya yi bayani game da raunukan kwanya da kuma dalilan da ke haddasa su.

ENG; Skull (A turance tana nufin kwanya)

Kwaramniya -

Tana nufin hayaniya mai ƙarfi ko girgiza kunne.

Misali; An ji kwaramniya a kasuwa lokacin da mutane suka taru.

ENG; Large noise (A turance tana nufin kwaramniya)

Kwaranga -

Tana nufin matakala da ake hawa daga ƙasa zuwa sama, musamman a gida ko itace.

Misali; Ya hau kwaranga domin ya kai kayan bene na biyu.

ENG; Ladder (A turance tana nufin kwaranga)

Kwarankwatsa -

Tana nufin sauti mai ƙarfi tare da hayaƙi da ake ji a lokacin hadari ko yayin da ake ruwan sama.

Misali; Yara sun tsorata da kwarankwatsa yayin da ruwan sama ya fara.

ENG; Thunder (A turance tana nufin kwarankwatsa)

Kwarara -

Tana nufin zubar abu da yawa ko yin abu sosai.

Misali; Tun safe ake kwarara ruwan sama.

ENG; Do much of (A turance tana nufin kwarara)

1 27 28 29 30 31 33