Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kwaleji - Tana nufin makaranta musamman ta gaba da sakandire.
Misali; Idan matasa suka shiga kwaleji suna jin kansu.
ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwaɓa - Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya.
Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin.
ENG; Mix Something (A turance tana nufin kwaɓa)
Kwaɗayi - Tana nufin tsananin son cin abu ko yin abu.
Misali; Tun da ta fara kwaɗayi na san tana da juna biyu.
ENG; Craving/ Yearning (A turance tana nufin kwaɗayi)
Kwaɗo - Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa.
Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu.
ENG; Frog (A turance tana nufin kwaɗo)