Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kwaf - Tana nufin kofi ko moɗa.
Misali; Inna ta siyo sabon kwaf mai launin shuɗi da fari.
ENG; Cup (A turance tana nufin kwaf)
Kwagiri - Tana nufin sandan da dattijai da attajirai suke amfani da shi idan suna tafiya.
Misali; Alhaji Lado yana amfani da kwagiri sama da shekara goma da na san shi.
ENG; Walking Stick (A turance tana nufin kwagiri)
Kwaikwaya - Tana nufin yin abu kamar yanda na asali yake.
Misali; Habu kukan doki yake kwaikwaya da na mage.
ENG; Imitate (A turance tana nufin kwaikwaya)
Kwaleji - Tana nufin makarantar gaba da firamare ko gaba da sakandire.
Misali; Duk wanda zai shiga kwaleji sai ya yi jarrabawa.
ENG; College (A turance tana nufin kwaleji)
Kwaɓa - Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya.
Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin.
ENG; Mix Something (A turance tana nufin kwaɓa)
Kwaɗayi - Tana nufin tsananin son cin abu ko yin abu.
Misali; Tun da ta fara kwaɗayi na san tana da juna biyu.
ENG; Craving/ Yearning (A turance tana nufin kwaɗayi)
Kwaɗo - Tana nufin wata dabba da ke rayuwa a ruwa kuma da doron ƙasa.
Misali; Tahir ya ga kwaɗo a bakin kwatar da ke ƙofar gidansu.
ENG; Frog (A turance tana nufin kwaɗo)