Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kusu - Tana nufin ɓera. Misali; Na ga kusu a cikin ɗakin ajiya, dole sai mun sa magani. ENG; Rat/Mouse (A turance tana nufin kusu)
Kusurwa - Tana nufin kwana. Misali; Na ajiye adakar a kusurwar ɗakin da muke kwana. ENG; Corner (A turance tana nufin kusurwa)
Kutsa - Tana nufin shiga da ƙyar. Misali; Ya kutsa cikin taron don ya ga gwamnan garinsu. ENG; Squeeze Through (A turance tana nufin kutsa)
Kuturta - Tana nufin lalurar da ke sa ƙuraje a jiki, ta canja siffar mutum gaba ɗaya kuma yatsu su lanƙawashe. Misali; Gwamnati ta daɗe da yaƙar cutar kuturta a ƙasar nan. ENG; Leprosy (A turance tana nufin kuturta)
Kuturu - Tana nufin mai ɗauke da lalurar kuturta. Misali; Ya ba wa kuturu sadaka a hanyarsa ta zuwa kasuwa. ENG; Leper (A turance tana nufin kuturu)
Kuwwa - Tana nufin ƙara. Misali; Yara na waje suna kuwwa saboda saukar ruwan sama na farko. ENG; Shouting (A turance tana nufin kuwwa)
Kuyanga - Tana nufin baiwa mace. Misali; Mallakar kuyanga sai masu hannu da shuni. ENG; Female Slave (A turance tana nufin kuyanga)
Kuza - Tana nufin zuba ruwa da yawa. Misali; Hindatu ta kuza ruwa a cikin shinkafar shi yasa ta yi luguf. ENG; Pour much water (A turance tana nufin kuza)
Kuzari - Tana nufin ƙarfi da lafiya. Misali; Jaririn yana da cikakken kuzari masha Allah. ENG; Showing Energy (A turance tana nufin kuzari)
Kuɓewa - Tana nufin ɗaya daga cikin tsirrai da ake shukawa a lambu, ana amfani da ita don yin miya da magani da sauransu. Misali; Tuwon Shinkafa da miyar kuɓewa muka ci yau da safe. ENG; Okra (A turance tana nufin kuɓewa)
1 23 24 25 26 27 33