Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Kurmi - Tana nufin ƙungurmin daji.
Misali; Jami'an tsaro sun kame ɓarayin da ke kurmi gaba ɗaya.
ENG; Thick Forest (A turance tana nufin kurmi)
Kurna - Tana nufin bishiya mai ƙaya mau ɗauke da ƙananan 'ya'ya masu zaƙi waɗanda ake sha.
Misali; 'Ya'yan kurna suke sha kullum idan sun je makaranta.
ENG; A thorny tree with edible berries (A turance tana nufin kurna)
Kurtu - Tana nufin ƙaramin mazubi na duma.
Misali; Maharazu ya zuba tawada a cikin kurtu.
ENG; Small Round Gourd (A turance tana nufin kurtu)
Kurum - Tana nufin kawai.
Misali; Kwano ɗaya kurum ta isa kowa ya ƙoshi.
ENG; Only (A turance tana nufin kurum)
Kururuwa - Tana nufin ihu da ƙarfi.
Misali; Sadiƙ yana da rowa idan aka ɗauki abinsa kururuwa yake.
ENG; Shouting (A turance tana nufin kururuwa)
Kusa - Tana nufin dab da.
Misali; Ana siyar da wainar gero a kusa da gidanmu.
ENG; Near (A turance tana nufin kusa)
Kushe - Tana nufin faɗar aibu ko ƙaƙalo laifin abu.
Misali; Duk yanda abu ya kai da kyau mahassada sai sun kushe shi.
ENG; Find Fault (A turance tana nufin kushe)
Kushewa - Tana nufin kabari.
Misali; An kai ta kushewa tun safe da aka yi jana'izarta.
ENG; Grave (A turance tana nufin kushewa)
Kushin - Tana nufin kujerar bature.
Misali; Hedimasta yana zaune a kan kushin ɗin ofishinsa a lokacin da muka kai masa ziyara.
ENG; Cushion (A turance tana nufin kushin)
Kuskure - Tana nufin yin abu ba daidai ba.
Misali; Idan mutum ya yi kuskure ya kamata a yi masa afuwa.
ENG; Failure (A turance tana nufin kuskure)