Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Kunkuru - Tana nufin wata dabba mai rayuwa a ruwa ko a doron ƙasa ko kuma guri mai danshi, tana tafiya a hankali kuma yana rayuwa mai tsayi. Misali; Kunkuru yana iya rayuwa sama da shekaru tamanin ba doron ƙasa. ENG; Tortoise (A turance tana nufin kunkuru)
Kunne - Tana nufin gaɓar da ake ji da ita. Misali; Yara na yawan yin ciwon kunne musamman lokacin sanyi. ENG; Ear (A turance tana nufin kunne)
Kuntigi - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa. Misali; Na jiyo kiɗan kuntigi a ƙofar gidan maigari. ENG; Small one-stringed plucked musical instrument (A turance tana nufin kuntigi)
Kuntu - Tana nufin bargo launin ruwan ƙasa wanda sojoji suke amfani da shi. Misali; An raba musu kuntu a ranar da suka shiga daji don yaƙi da 'yan ta'adda. ENG; Brown blanket used by army personnel (A turance tana nufin kuntu)
Kuntukuru - Tana nufin ɗaya daga cikin kayan kiɗan Hausawa. Misali; Na jiyo sautin kuntukuru, da alama an fara wasan. ENG; Small bowl-shaped drum which is hung from the neck and beaten with small flexible sticks (A turance tana nufin kuntukuru)
Kunu - Tana nufin abin sha wanda ake yi da gari ko markaɗaɗɗen gero mai ƙunshe da kayan ƙamshi da tsamiya ko kanwa. Misali; An dama wa mai jego kunu. ENG; Gruel made of guinea-corn or millet flour (A turance tana nufin kunu)
Kunya - Tana nufin kawaici ko jin nauyin aikata lefi ko haɗa ido da mutane. Misali; Yarinyar tana da kunya da ɗa'a. ENG; Modesty (A turance tana nufin kunya)
Kunya - Tana nufin dogwayen tudu-tudun da ke gona. Misali; Iro ya noma kunya bakwai yau a gona. ENG; Ridge-row on farm (A turance tana nufin kunya)
Kura - Tana nufin wata dabbar daji mai cin ɗanyen nama. Misali; Mafarautan sun kamo kura. ENG; Hyena (A turance tana nufin kura)
Kuratandu - Tana nufin mazubin kwalli wato mazubin da ake adana kwalli a ciki. Misali; Inna Hajjo ta kawo wa mai jego kyautar kurantandu cike da farin kwalli. ENG: Small hide container (A turance tana nufin kuratandu)
1 20 21 22 23 24 33