Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Karya - Tana nufin macen kare.
Misali; Wata karya ce ta haihu a bayan layinmu.
ENG; Bitch (A turance tana nufin karya)
Karya - Tana nufin ɓalla abu ko raba shi gida biyu.
Misali; Yaran sun karya kujerun ajin su.
ENG; Break (A turance tana nufin karya)
Karɓa - Tana nufin riƙewa ko yarda.
Misali; Duk hukuncin da aka yanke masa dole ya karɓa don ya yi gagarumin laifi.
ENG; Accept/Received (A turance tana nufin karɓa)
Kasada - Tana nufin yin abu mai hatsari ko ganganci.
Misali; Bin hanyar nan kasada ne saboda akwai 'yan ta'adda a wajen.
ENG; Risk (A turance tana nufin kasada)
Kasala - Tana nufin mutuwar jiki ko rashin jin ƙarfin jiki.
Misali; Jin kasala na ɗaya daga cikin alamomin juna biyu.
ENG; Lack of Energy (A turance tana nufin kasala)
Katifa - Tana nufin abin kwanciya mai laushi.
Misali; An siyowa amarya sabuwar katifa.
ENG; Mattress (A turance tana nufin katifa)
Katsalandan - Tana nufin shiga abin da bai shafi mutum ba ko shisshigi.
Misali; Makwabcinsa yana yawan yi masa katsaladan a al'amuran shi.
ENG; Intrusiveness (A turance tana nufin katsalandan)
Katse - Tana nufin yankewa ko tsayar da abu.
Misali; Idan aka katse min bacci ciwon kai yake sa ni.
ENG; Cut Off (A turance tana nufin katse)
Kauci - Tana nufin wani tsiro da yake fitowa a jikin bishiya, kuma yana fitowa ne sakamakon sauka da tsuntsaye ke yi daga wata bishiyar zuwa wata.
Misali; Ana amfani da kauci wajen magungunan cututtuka da dama.
ENG; A parasitic plant which grows on trees (A turance tana nufin kauci)
Kauri - Tana nufin abin da ba siriri ba ko kuma wanda ba ruwa-ruwa ba.
Misali; Kunun da ta dama ya yi kauri sosai, sai an ƙara ruwa.
ENG; Thickness (A turance tana nufin kauri)