Ƙage -
Tana nufin zargin mutum da wani abu da be aikata ba ko ba tare da hujja ba.
Misali: An yi masa ƙagen ya saci kuɗi.
ENG: False accusation (A turance tana nufin ƙage)
Ƙaho -
Tana nufin wani abu mai ƙarfi da ke fitowa a kan dabba kamar shanu, awaki ko tumaki.
Misali: Shanu suna da ƙaho a kansu.
ENG: Horn (A turance tana nufin ƙaho)
Ƙaimi -
Tana nufin wani abu mai kaifi da ke fitowa a ƙafar dabba (musamman zakara ko wasu tsuntsaye) da suke amfani da shi wajen kare kai ko faɗa.
Misali; Zakara yana amfani da ƙaiminsa wajen faɗa.
ENG; Spur (A turance tana nufin ƙaimi)
Ƙaiƙayi -
Tana nufin jin son sosa wani guri ko sashen jiki.
Misali: Yana jin ƙaiƙayi a hannunsa bayan sauro ya cije shi.
ENG: Itching (A turance tana nufin ƙaiƙayi)
Ƙalau - Tana nufin sosai ko matuƙa.
Misali; Shanyin ya yi sanyi ƙalau sai an sake dafa shi.
ENG; Very (A turance tana nufin ƙalau.)
Ƙam-ƙam - Tana nufin riƙe abu da ƙarfi.
Misali; Ya kamata mu riƙe addini ƙam-ƙam domin inganta rayuwarmu.
ENG; Tightly (A turance tana nufin ƙam-ƙam)
Ƙamfa - Tana nufin rashin wani abu ko ƙarancinsa.
Misali; An samu ƙamfar ruwa a ƙauyen saboda rashin zuwan ruwan sama.
ENG; Lack/Shortage (A turance tana nufin ƙamfa)
Ƙamshi - Tana nufin shaƙar daddaɗar iska.
Misali; Furen nan yana da ƙamshi mai daɗi.
ENG; Fragrant (A turance tana nufin ƙamshi)
Ƙamusu - Tana nufin littafin da ke ƙunshe da rubutattun kalmomi da ma'anarsu.
Misali; Dalibi ya duba ƙamus domin ya fahimci ma’anar kalmar.
ENG; Dictionary (A turance tana nufin ƙamusu)
Ƙandare - Tana nufin bushewa ko zama babu ruwa.
Misali; Rijiyar ta ƙandare saboda tsananin zafi.
ENG; Become dry (A turance tana nufin ƙandare)