Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙulumi - Tana nufin mutum mai tsananin rowa wanda ba ya son bayarwa ko taimakon wasu da abin da yake da shi.
Misali: Mutane ba sa son halin ƙulumi domin yana hana mutum kyautatawa da taimakon jama'a.
ENG: Stingy Person (A turance tana nufin ƙulumi).
Ƙuma - Tana nufin wani ƙaramin ƙwaro mai tsalle wanda ke rayuwa a jikin dabbobi ko mutane, yana tsotsar jini kuma yana iya haddasa ƙaiƙayi.
Misali: Karen ya kamu da ƙuma, shi ya sa yake ta susa kullum.
ENG: Flea (A turance tana nufin ƙuma)
Ƙumba - Tana nufin farce.
Misali: Ya yanke ƙumbarsa domin ta yi tsawo sosai kuma tana ji masa ciwo.
ENG: Fingernail (A turance tana nufin ƙumba).
Ƙumbiya-ƙumbiya - Tana nufin yin magana ko bayani cikin karkacewa ba tare da zuwa kan ainihin batu kai tsaye ba.
Misali: Ka daina ƙumbiya-ƙumbiya ka faɗi abin da kake nufi kai tsaye.
ENG: Inability to come to the point; beating around the bush (A turance tana nufin ƙumbiya-ƙumbiya).
Ƙuna - Tana nufin tsananin zafi, musamman zafin rana, wuta, ko yanayi mai matuƙar zafi.
Misali: Yau rana ta yi matuƙar ƙuna da alama za a yi ruwan sama.
ENG: Great Heat (A turance tana nufin ƙuna)
Ƙunci - Tana nufin halin rashin jin daɗi ko zafin rai da mutum ke shiga.
Misali: Zuciya na ƙunci idan ta rasa makusancinta.
ENG: Bad Temper (A turance tana nufin ƙunci).
Ƙundu - Tana nufin wani ɓangare na cikin tsuntsaye, musamman kaji, wanda ke taimakawa wajen niƙa abinci kafin ya ci gaba da narkewa.
Misali: Wasu mutane suna son cin ƙundu idan aka dafa kaza.
ENG: Gizzard (A turance tana nufin ƙundu)
Ƙungiya - Tana nufin taron mutane da suka haɗu domin wata manufa guda, aiki, ko amfani na bai ɗaya.
Misali: Ya shiga ƙungiyar matasa domin ya ba da gudummawa wajen cigaban al'umma.
ENG: Society / Union (A turance tana nufin ƙungiya)
Ƙungurmi - Tana nufin tsanani ko tantagarya.
Misali: Sun shiga cikin ƙungurmin daji domin yin farauta.
ENG: Bare State (A turance tana nufin ƙungurmi).
Ƙunsa - Tana nufin kasancewar wani abu a cikin wani abu.
Misali: Wannan littafin tarihin Hausawa ya ƙunsa.
ENG: Contain (A turance tana nufin ƙunsa).