Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙugi - Tana nufin ƙara.
Misali: Ana jin ƙugin cikinsa saboda ciwon da yake masa.
ENG: Groaning (A turance tana nufin ƙugi)
Ƙugiya - Tana nufin lanƙwasasshen ƙarfen da ake amfani da shi wajen rataya, kama abu, ko jawo wani abu.
Misali: Ya rataye rigarsa a ƙugiyar da ke jikin bango.
ENG: Hook (A turance tana nufin ƙugiya)
Ƙwadago - Dukkan wani irin aikin da mutum zai yi a biya shi kudi a matsayin lada ko albashi.
Ƙwaƙƙwafi - Bin diddigi domin gano wani ɓoyayyen al'amari.