Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ƙoƙe - Tana nufin dusashewa ko raguwar launi.
Misali: Launin zanen ya ƙoƙe saboda yawan wankewa da take yi.
ENG: Fade (A turance tana nufin ƙoƙe)
Ƙoƙi - Tana nufin matar Gizo, wanda sanannen jarumi ne mai dabara a tatsuniyoyin Hausawa. Ana yawan ambatonta a cikin labaran gargajiya tare da Gizo.
Misali: A tatsuniyar jiya, Ƙoƙi ta taimaka wa Gizo wajen warware matsalolinsa.
ENG: Wife of Gizo (a trickster hero in Hausa folklore) (A turance tana nufin Ƙoƙi)
Ƙoƙi-ƙoƙi - Tana nufin wani irin ƙwaro kore mai dogayen ƙafafu da hannaye masu kama da mutum mai yin addu’a.
Misali: Yara sun ga ƙoƙi-ƙoƙi a jikin bishiya suna kallon yadda take motsi.
ENG: Praying Mantis (A turance tana nufin ƙoƙi-ƙoƙi)
Ƙoƙo - Tana nufin ƙaramar ƙwarya da ake amfani da ita wajen shan ruwa, nono, ko mulmula tuwo ko adana wasu abubuwa.
Misali: Ta ɗebo nono a cikin ƙoƙo za ta kai wa maƙota.
ENG: Small Calabash (A turance tana nufin ƙoƙo)
Ƙoƙuwa - Tana nufin saman hula.
Misali: An ƙawata ƙoƙuwar hular da zare mai launi.
ENG: Top of Cap (A turance tana nufin ƙoƙuwa)
Ƙubaka - Tana nufin wajen saka tazuge da ke saman wando.
Misali: Telan ya gyara ƙubakar wandon domin igiyar ta shiga sosai.
ENG: Hem for trouser string (A turance tana nufin ƙubaka)
Ƙuda - Tana nufin ƙaramin ƙwaro mai tashi wanda ake yawan samu a kusa da abinci ko ƙazanta.
Misali: Ƙuda na yawan taruwa a kan abincin da aka bari a buɗe.
ENG: Fly (A turance tana nufin ƙuda)
Ƙudundune - Tana nufin kwanciya a nannaɗe ko a dunƙule saboda jin sanyi, ko ciwo.
Misali: Yaron ya ƙudundune a kan tabarma saboda yana jin sanyi.
ENG: Lie curled up (A turance tana nufin ƙudundune)
Ƙudura - Tana nufin yanke shawara da cimma matsayar yin wani abu bayan an yi tunani.
Misali: Ya ƙudura a ransa cewa zai ci gaba da karatunsa duk da tarin ƙalubalen da yake fuskanta.
ENG: Decide (A turance tana nufin ƙudura)
Ƙufula - Tana nufin saurin fushi.
Misali; Ƙufula ya yi har ta kai ga ya mare shi.
ENG; Quick-Tempered (A turance tana nufin ƙufula)