Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ridge-row on farm - A turance tana nufin kunya.
Misali; Iro ya noma kunya bakwai yau a gona.
HAU; Kunya (Tana nufin dogwayen tudu-tudun da ke gona)
Rinse - A turance tana nufin ɗauraye.
Misali; Na ɗauraye kwanon kafin in zuba abinci.
HAU; Ɗauraye (Tana nufin sa ruwa a sake wanke abu)
Risk - A turance tana nufin kasada.
Misali; Bin hanyar nan kasada ne saboda akwai 'yan ta'adda a wajen.
HAU; Kasada (Tana nufin yin abu mai hatsari ko ganganci)
Risk Managers Association of Nigeria (RIMAN) - Ƙungiyar Manajojin Tsagaita Asara Ta Najeriya
Risk, Accident - A turance tana nufin haɗari.
Misali; 1. Shaƙar hayaƙin taba na da haɗari ga lafiya.
2. Ya samu karaya sakamakon haɗarin mota.
HAU; Haɗari (Tana nufin abin da zai iya cutarwa, ko tsautsayin da ke faruwa a kan titi)
Rivalry/Opponent - A turance tana nufin hamayya.
Misali; Abokan hamayya ne su a siyasa shi yasa ba sa ga maciji.
HAU; Hamayya (Tana nufin kishi ko takun saƙa)
River - A turance tana nufin gulbi.
Misali; Indo da ƙawayenta sun tafi gulbi yin wanki.
HAU; Gulbi (Tana nufin kwari da ruwa yake taruwa)
River - A turance tana nufin kogi.
Misali; An tsinci jariri a bakin kogi ranar Asabar.
HAU; Kogi (Tana nufin ruwa mai gudana)
Road Transport Employers’ Association of Nigeria (RTEAN) - Ƙungiyar Direbobi Ta Najeriya
Road/ Path - A turance tana nufin hanya.
Misali; Gwamnati ta gina hanya a tsakanin ƙauyukan guda biyu.
HAU; Hanya (Tana nufin guri ko inda ake wucewa)