Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Reason - A turance tana nufin hujja.
Misali; Sun yi rashin nasara saboda ba su da ƙwaƙƙwarar hujja a shari'ar.
HAU; Hujja (Tana nufin dalili)
Reckoning up the good and bad deeds of a person on judgement day - A turance tana nufin hisabi.
Misali; Muna fatan samun dace a ranar hisabi.
HAU; Hisabi (Tana nufin lissafa ayyukan mutum masu kyau da marasa kyau a ranar lahira)
Red - A turance tana nufin ja.
Misali; Akwai launin ja a jikin kayan da ya saka.
HAU; Ja (Tana nufin launin ja)
Reform - A turance tana nufin jaddada.
Misali; Shugaban makarantarmu ya jaddada mana muhimmancin taron iyayen yara da za a yi gobe.
HAU; Jaddada (Tana nufin tabbatarwa)
Refuse - A turance tana nufin bola.
Misali; Motar ɗiban shara ta kwashe bolar bakin kasuwa.
HAU; Bola (Tana nufin shara ko kayan da aka gama amfani da su waɗanda za a zubar)
Relationship - A turance tana nufin dangantaka.
Misali;Akwai dangantaka tsakanin angon da amaryar.
HAU; Dangantaka (Tana nufin alaƙa)
Relax, Enjoy - A turance tana nufin hole.
Misali; Yau za mu hole mu sha shagali saboda an ɗaura auren ƙawarmu.
HAU; Hole (Tana nufin hutu da jin daɗi)
Religious Impurity - A turance tana nufin janaba.
Misali; idan mutum na da janaba, ba zai yi sallah ba dole sai ya yi tsarki.
HAU; Janaba (Tana nufin rashin tsarki a addinin musulunci sakamakon biƙi, haila, kusantar iyali da sauransu)
Kishiyarta; Tsarki
Remaining particles - A turance tana nufin diddiga.
Misali; Naman ya ƙare saura diddiga.
HAU; Diddiga (Tana nufin sauran abu ko ɓirɓishinsa)
Removal of things to another location - A turance tana nufin jido.
Misali; Mun jido kayan daga tsohon gida zuwa sabo.
HAU; Jido (Tana nufin ɗebo kaya daga wani guri zuwa wani gurin)