Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Emir’s Bodyguard - A turance tana nufin dogari.
Misali; Tanimu dogari ne a masarautar Kano.
HAU; Dogari (Tana nufin masu ba wa sarki tsaro)
Emphasizes blackness - A turance tana nufin ƙirin.
Misali: Hadari ya haɗo, gari ya yi baƙi ƙirin.
HAU: Ƙirin (Tana nufin ƙarfafa ko bayyana baƙin launi sosai)
Empty container - A turance tana nufin fanko.
Misali; Gwangwanin fanko ne.
HAU; Fanko (Tana nufin babu komai)
End - A turance tana nufin ƙarshe.
Misali: Fim ɗin da muke gani ya zo ƙarshe.
HAU: Ƙarshe (Tana nufin kankat wato daga nan ba ƙari ko cigaba).
Endurance/Patience - A turance tana nufin jimiri.
Misali; Duk wanda ya yi jimirin yin aiki zai samu kyakkyawan sakamako.
HAU; Jimiri (Tana nufin haƙuri da juriya)
Endure - A turance tana nufin jure.
Misali; Ta jure mugayen halayensa tsawon shekaru.
HAU; Jure (Tana nufin dauriya)
Energy Commission of Nigeria (ECN) - Hukumar makamashi Ta Najeriya
Enmity - A turance tana nufin gaba.
Misali; Ai sun daɗe suna gaba da juna saboda dalilin da bai kai ya kawo ba.
HAU; Gaba (Tana nufin daina yi wa juna magana)
Environmental Health Officers Association of Nigeria (EHOAN) - Ƙungiyar malaman tsabtar mahalli ta Najeriya
Envy - A turance tana nufin hassada.
Misali; Daga cikin munanan ɗabi'u akwai hassada da kuma ƙarya.
HAU; Hassada (Tana nufin jin ƙyashi ko baƙin ciki idan wani ya samu abin alkhairi ko cigaba ko ɗaukaka da sauransu)