Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Pride - A turance yana nufin alfahari. Misali; Mata suna da yawan alfahari. HAU; Alfahari (Jin isa ko fifiko akan wasu)
Primary School - A turance tana nufin firamare. Misali; Farida ta shiga firamare. HAU; Firamare (Tana nufin matakin farko na karatun boko)
Prison - A turance tana nufin kurkuku. Misali; Jami'an sun tafi da masu laifin kurkuku. HAU; Kurkuku (Tana nufin inda ake ajiye masu laifi, waɗanda aka yankewa hukunci da masu jiran hukunci)
Private Discussion - A turance tana nufin ganawa. Misali; Shugaban makarantar na ganawa da malamai a ofishinsa. HAU; Ganawa (Tana nufin tattaunawar sirri ko ta musamman)
Program - Shiri, Gidauniya
Project - Gidauniya, Aiki
Project Development Institute (PDI) - Cibiyar Naƙaltar Bunƙasa Ayyuka
Property - A turance tana nufin kadara. Misali; Sun buƙaci ya kawo takardun wata kadara kafin su ba shi rancen kuɗi. HAU; Kadara (Tana nufin kaya masu daraja ko kayan kuɗi)
Prophet - A turance yana nufin wanda Allah ya aiko. Misali; Shugaban annabawa shi ne annabi Muhammad (S.A.W) HAU; Annabi (Wanda Allah ya aiko da saƙon addini)
Prostitute - A turance tana nufin karuwa. Misali; Ku karanta ƙissar karuwa da karen da ta ba wa ruwa, akwai darasi. HAU; Karuwa (Tana nufin mace mai zaman kanta)
1 6 7 8 9 10